Hanyoyi 5 Da Ake Samun Kudi Dasu A Internet | Thegoldengist.Com

 Hanyoyi 5 Da Ake Samun Kudi Dasu A Internet

Abun daya zama ruwan dare yanzu shine Yadda ake samun a internet, idan har kana shiga internet zaka samun irin wadannan sakonni agurare dayawa kamar Facebook, Watsapp, Instagram, Youtube da sauransu. Abu mafi wuya shine sanin hanyar data dace wajen neman kudi a internet. Ayau insha allahu zamu kawo wasu hanyoyi guda 5 wanda zaka iya samun kudi dasu a internet.

Samun kudi a internet ba abune mai sauki ba, Domin tamkar neman abin daba kasani bane ba. Amma idan kasan hanyoyin samun kudi a internet zaka iya kwana kana bacci yayin dakake samun  kudi. Amma sanin hanyar data shine babban aiki wanda yau zamu hanyoyi tabbatattu wanda idan kayi amfani dasu to tabbas zaka samu kudi a internet.


Jerin Hanyoyi 5 Wanda Zaka Samu Kudi Dasu A Internet


(1) Hanya tafarko itace Blogging wato mallakar Website ko Blog domin samun  kudi dashi a internet, Wannan hanya babu shakka acikinta wajen samun Online, Idan kana bukatar samun samun kudi zaka iya free website a Blogger kokuma wanda zaka kashe kudi kadan wajen budewa a Wordpress. Daga lokacin daka bude Website zaka nemo wani abu wanda zaka iya rubutawa a wannan website domin jawo mutane, Dazarar mutane sunfara shiga wannan shiga wannan website zaka iya Join da Google Adsense ko Propeller Ads domin samun kudi.
(2) Hanya tabiyu itace Youtube wajen dayayi suna wajen kallon videos, Zaka iya samun kudi a internet idan kabude channel a Youtube. Zaka iya bude channel a youtube kyauta idan kasamu Subscribers 1000 dakuma awa 4000 youtube zata duba wannan channel idan bai saba da dokar youtube ba zaka shiga tsarin daza kana samun kudi da wannan channel. Wannan hanya tana da suki sosai wajen neman kudi online domin zaka iya kirkirar video kadora a youtube kana samun kudi dashi sama da shekara goma.
(3) Hanya ta uku itace Social Media Marketing wato kasuwancin kafafen sadarwa na Internet, Wannan kasuwanci yanada sauki idan ka iyashi wato zaka shiga manyan shafukan sadarwa na internet kamar Facebook, Instagram, Watsapp, Twitter da sauransu. Zaka bude shfi ko profile sannan katara mutane daga nan sai kanemi wani abu dazai kawo maka kudi sai kana talla tashi a wadannan shafuka.


Yadanganta da abin dakake son tallatawa wato nakane kokuma na wani kamfani ne koma dai yaya kayi zaka iya samun kudi da wadannan shafuka matukar kana da mutane masu yawa.
(4) Hanya ta hudu itace Affiliate Program wato tallata kayan wani kampani ko wani mutum idan kasayar kasamu wani abu daga ciki. Wannan hanya ana samun kudi da  ita sosai a internet domin zaka iya samun sama da dubu hamsin (50k) cikin wata daya batare daka bude website ko blog ba, Akwai sanannun kamfani dasukayi suna a nigeria wanda suke da tsarin affliate program kamar su Jumia, dadai sauransu.(5) Hanya ta biyar itace itace Freelanceing wato Kodago a internet, Zaka iya samun da wannan hanya idan ka iya wani aiki wanda ake nema a yanar gizo. Ana samun kidi da freelancing ta hanyar shiga manyan website dasuke da wannan tsari domin neman aiki. Wato zaka shiga wasu neman aiki a internet inda zaka iya yin aikin abiyaka kudi cikin kankanin lokaci. Idan kana da wani dakasan kakware akansa zaka iya samun aiki agurare kamar Facebook kullum. Akwai ayyuka da ake yawan neman wanda suka iyasu kamar Website Design, Adsense Approval, SEO, da sauransu.Wadannan sune hanyoyi guda biyar dazaka iya neman kudi dasu a internet cikin sauki. Wadannan hanyoyi idan kaga baka samu kudi dasu ba to baka bisu ba, Abin nufi shine duk hanya daka dauka domin kudi da ita to akwai bukatar kamaida hankali akanta sosai. Wannan shine karshen wannan post idan kunji dadin wannan rubuta kuyi Share zuwa wasu gurare, Mungode.


Post a Comment

0 Comments